Yau Ce Ranar Bikin Matasa Ta Duniya

Hadimin Shugaban N-Power Ya Yaba Da Yadda Matasa Ko Son Rungumar Shirin N-Power A Jihar Taraba

Yau ranar Asabar 12 ga watan Agusta ranace da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin bikin ranar matasan duniya.

Wannan rana dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa akwai matasa Miliyan 73 dake fama da rashin aikin yi.

A sakon babban sakataren MDD na wannan rana, António Guterres, ya ce ya dauki kudirin kawo karshen matasalar da matasa ke fuskanta a sassa na duniya, yana kuma fatan samun hadin kan cimma wannan kuduri daga matasa.

Bukin dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da matasa a sassa daban-daban na duniya ke fuskantar kalubale ta fuskoki da dama.

Majalisar Dinkin Duniya ta zartar da kudurori 15 don inganta zamantakewar matasa da ci gabansu, wadanda suka hada da samar da ilimi da ayyukan yi da kawar da talauci da Yunwa da samar da lafiya da kuma kawo karshen shan mugayen kwayoyi.

Najeriya dai na daga cikin kasashen da ke daukar irin wadannan matakai, kamar yadda farkon hawa kan karagar mulki gwamnatin shugaba Buhari, ta bayyana aniyarta na samar da ayyukan yi ga matasa a matsayin daya daga cikin kudurorinta.

Yanzu haka dai gwamnatoci da Majalisar Dinkin Duniya sun tashi tsaye wajen fuskantar matsalolin da matasa ke fuskanta.

Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin daga Legas.

Your browser doesn’t support HTML5

Yau Ce Ranar Bikin Matasa Ta Duniya - 3'31"