Shugaban karamar hukumar Yola ta arewa, Kansiloli da magoya bayansa sun yi kutse a harabar sakatariyar duk da killaceta da jami’an ‘yan sanda dauke da makamai da motocin tarwatsa tarzoma masu fesa ruwan zafi da toka mai sa hawaye da aka girke a wurin.
Dambarwar da ta dabaibaye shugabanncin karamar hukumar Yola ta Arewa ta dauki sabon salo bayan karewar wa’adin dakatar da shugaban karamar hukumar AlhAJI Mahmud Abba na tsawon makonni shida ranar Ishirin da biyar na watan da ya gabata.
Abinda da ya harzuka shugaban karamar hukumar da magoya bayansa shine kyale bangaren da mataimakinsa Mr, George Raphael ke shugabanta na rikon kwarya da gwamnatin jihar ta nada shiga da gudanar da taro a zauren majalisar inji Alhaji Mahmud Abba wanda ya bayyana da cin fuska ne ga zababben shugaba karkashin mulkin dimukaradiyya.
Da yake bayanin dalilin killace sakatariyar, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa SP Abubakar Othman ya ce sun dau matakin killace harabar ne don kaucewa jayayya tsakanin bangarorin biyu kan shugabancin karamar hukuma ta kazance har a kai ga karya doka da oda da basu damar warware rikicin a gaban kotu.
Bincike da Murya Amurka ta gudanar ta gano cewa hukumar kula da kananan hukumomi ta jihar Adamawa ta hanun sakataren dindindin Mr, Polycarp Ayuba ta umurci daraktocin karanmar hukumar Yola ta Arewa kada su yi hulda da Alhaji Mahmud Abba a wata wasika da ta rubuta ranar ishirin da shida ga watan Yuli na wannan shekarar kwana daya bayan karewar wa’adin dakatar da shi.
Shugaban majalisar kansilolin karamar hukumar Yol Buhari Yahuza ya ce da lauje cikin nadi saboda wasikar bata fayyace wa ta baiwa rikon shugabanci ba bayan karewar wa’adin dakatar da shugaban lokacin da ya ke yi wa wakilinmu fashin bakin wasikar.
Wakilinmu Muryar Amurka ya yi kokarin ya ji ta bakin sakataren dindindin na hukumar Mr, Polycarp Ayuba da mataimakin shugaban karamar hukumar George Raphael kan wannan batu ta wayar hanu da sakonnin kar ta kwana amma sun ki daukar wayoyinsu.
Saurari karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.
Facebook Forum