Farfasa Osinbajo, mukaddashin shugaban kasa ya amince da nada manyan sakatarori 21.Lamarin ya kara nuna yadda yake kara natsuwa cikin aiki ta yin sauye sauye da nade nade
Barrister Solomon Dalung ministan wasanni da matasa yace kafin shugaban kasa ya tafi jinya ya mika mulki wa mataimakinsa saboda haka yana da cikakken iko na shugaban kasar har sai Shugaba Buhari ya dawo ya sake rubuta wasika kafin ya karbi ikonsa. A yanzu yana da ikon yin abubuwan da ya keyi.
Sai dai a fahimtar wasu daga arewa na zama na damuwa ganin sunayen kan kunshi Yarbawa a kowane juyi.Umar Gombe dan jarida ne kuma yayi korafi akan sunayen. A ganinsa an yi magudi an saka Yarbawa da yawa.
Nada sakatarorin ya biyo bayan jarabawa ne da daraktoci fiye da dari uku suka yi domin cike wuraren manyan sakatarori 21. Saboda hakan ya zama wajibi ilimin fasaha da kimiya na zamani su taka rawa a nadasu.
Tsohon ma'aikacin gwamnati Tank Iya yace bai ga wani aibu a nada manyan sakatarorin ba. Yace da ya duba sunayen ya ga mutane daga Katsina, Sokoto har da Birnin Tarayya, Abuja. An yi tunane an raba hannu ba tare da son zuciya ba.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum