Rahotanni da muka samu da dumi duminsu na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun kone garin Yumbuli kurmus.
Garin Yumbuli yana cikin karamar hukumar Madagali ne kuma yana kan iyaka da dajin Sambisa inda 'yan Boko Haram suka yi kakagida.
Harin na yau shi ne na hudu cikin mako guda da 'yan Boko Haram zasu kai a yankin na Madagali.
Shugaban karamar hukumar Madagali shi ya yiwa Muryar Amurka karin bayani daga baya kuma watakila jami'an tsaro zasu bada nasu.
Ta bakin Alhaji Yusuf Muhammad shugaban karamar hukumar Madagali abun da suka tarar abun takaici ne kuma abun kuka ne saboda duk garin gaba daya 'yan Boko Haram suka kone. Sun kone gidagensu da abincinsu da dabbobinsu da duka kayansu. Babu wanda ya fita da komi illa abun da yake sanye dashi.
Alhaji Yusuf yace babu wanda aka kashe saboda duk sun gudu sun hau duwatsu. A jihar Adamawa Madagali ce ta fi shan wahala a hannun 'yan Boko Haram. Kullum sai an kashe mutane a yankin.
Inji Alhaji Yusuf mutanensu basu iya zuwa gona. Ya roki gwamnati ta taimaki mutanensu su kuma kara dakarun tsaro ba jiye sojoji hamsin ba kawai. Yace a kawo sojoji da yawa domn suna makwaftaka da dajin da 'yan ta'addan suke.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Facebook Forum