Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Kutsa Ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Maiduguri


Wasu sojojin Najeriya a Maiduguri
Wasu sojojin Najeriya a Maiduguri

Yau da misalin karfe biyar na safiya wasu sojojin Najeriya suka kutsa cikin ofishin Majalisar Dinkin Duniya ko MDD dake Maiduguri ba tare da izinin ba

Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta tabbatar da cewa rundunar sojojin Najeriya ta kutsa cikin ofishinta dake Maiduguri da misalin karfe biyar na asuba ba tare da samun izinin ba.

A sanarwar da ta aikawa manema labarai MDD ta ce sojojin sun afka ofishinsu ne inda suka kuma gudanar da bincike ba tare da shsaida masu manufarsu ba.

To saidai jama'ar gari na raderadin akwai wani abun dake faruwa ne ko kuma an boye wasu 'yan ta'adda ciki. Amma wani jami'in Majalisar Dinkin Duniyan Edward Kalo da gwamnatin Najeriya suna hada kai tare bisa wannan lamarin. Ana kyautata zato daga bisani zasu bayyana abun dake faruwa.

Ita dai MDD ta damu ne da kare al'umma da wadanda suka fada cikin halin kakanikayi na shiyar arewa maso gabashin Najeriya.

Rundunar sojin Najeriya dake cikin birnin Maiduguri ta mayar da martani akan abun da ya faru. Tace abun da ya faru ba sabon abu ba ne Daga lokaci zuwa lokaci ta kan aiwatar da bincike cikin anguwanni a kokarinsu na zakulo 'yan kungiyar Boko Haram wanda ya basu nasara da dama a wasu wuraren. Yawaitar hare haren da Boko Haram ke gudanarwa cikin 'yan kwanakin nan ya sa sojojin daukan matakin.

Inji sojojin sun gudanar da bincken ne bisa ga rahoton siri da suka samu na cewa wasu 'yan ta'adda suna anguwar. Dalili ke nan da suka yiwa gidaje 30 kawanya ciki ko har da gidan MDD. Sun gudanar da bincike amma basu kama kowa ba.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG