Shugabar hukuma mai kula da al’amuran ‘yan Najeira dake kasashen waje Abike Dabiri-Erewa ta bayyana cewa ‘Yan Najeriyan da aka kwaso daga Sudan zasu sauka a tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Abike Dabiri ta bada wannan sanarwar ne ta wani sakon da ta wallafa a shafinta na twitter a jiya Laraba tace ‘yan Najeiyan da aka kwaso daga Sudan sun baro kasar Masar a cikin wani jirgin sojin saman Najeriya kuma ana sa ran zasu isa tashar jirgin da misalign karfe 11: 23 na daren jiya.
Sakon da ta rubuta a shafin nata yace “A karshe dai, sun kamo hanyar zuwa gida cikin jirgin sojin saman Najeriya mai lamba C-130H wanda ya tashi daga Aswan kuma ana sa ran zasu isa babbar tashar jiragen saman Najeriya na Nnamdi Azikiwe dake birnin Abuja da misalign karfe 11:23 na daren yau” Muna Addu’a Allah Ya kawo su lafiya”.
Idan ba’a manta ba, shugabar ta NIDCOM a ranar asabar, ta sanar da cewa ofishin jakadancin Najeriya a Masar yana shirye-shiryen biyan kudaden bisan ‘yan Najeriyan da suka makale akan iyyakar kasar.