Yarjejeniyar Nukiliyar Iran: Sauran Kasashen Duniya Sun Ce Ba Ta Mutu Ba Tukunna

  • Ibrahim Garba

Shugaba Donald Trump

A cigaba da cece-kucen da ake yi kan yarjejeniyar nukiliyar Iran, sauran kasashen duniya sun ce su kam su na nan daram cikin yarjejeniyar duk kuwa da janyewar da Amurka ta yi.

Bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya yanke shawarar janyewa daga yajejeniyar da kasashen duniya su ka cimma kan nukiyar Iran, sauran kasashen da su ka rattaba hannu kan yarjajjeniyar sun fadi yau Laraba cewa har yanzu su na cikin yarjejeniyar.

Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya gaya wa gidan rediyon RTL cewa yarjajjeniyar na nan daram. Ya ce Firaministan Faransa Emmanuel Macron da Shugaban Iran Hassan Rouhani za su yi jawabi a yau dinnan Laraba, kuma Ministocin Harkokin Wajen Faransa da Burtaniya da Jamus za su tattauna da jami’an gwamnatin Iran ranar Litini mai zuwa.

Baya ga wannan fafatukar da ake yi a diflomasiyyance, Ministocin Harkokin Wajen Jamus da na Rasha za su gana ranar Alhamis a birnin Moscow da na Iran don gabatar da shawararsu.

Ma’aikatar Harkokin Wajen China ta sha alwashin cigaba da mutunta yarjajjeniyar ta 2015 wadda ake kira JCPOA a takaice, sannan ta ce ta yi takaicin shawarar da Trump ya yanke ta ficewa.

Wata takardar sanarwar hadin gwiwa ta Kungiyar Tarayyar Turai, ta ce zuwa yanzu dai yarjajjeniyar ta JCPOA ta cimma burinta na tabbatar da cewa Iran ba ta gudanar da shirin nukiliya ba, kuma dage takunkumin da aka yi ma Iran ya inganta harkokin kasuwanci da diflomasiyya.

Wannan matsayin ya sha banban matuka da na Trump, wanda jiya Talata ya kira yarjajjeniyar, “mashiririyar yarjajjeniyar da ke amfanar bangare guda kawai, wadda sam bai kamata ace ma an taba yin irinta ba.”