Shugaban Amurka Donald Trump yace a yau Talata zai sanar ko Amurka zata fice a cikin yarjejeniyar kasa da kasa a kan shirin nukiliyar Iran kuma idan tayi hakan ta sake azawa kasar takunkumai karya tattalin arziki.
Trump ya sha suka yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2015 da ta ragewa Iran radadin takunkumai kana ita kuma Iran ta dakatar da shirin nukiliyarta, yana mai cewa yarjejeniyar wani "bala’I ne kawai."
Yace wannan bai hana Iran gwaje gwajen makamai masu lizzami ba ya kuma kara da cewa wannan yarjejeniya akwai wasu sharudda dangane da shirin Nukiliyar da zassu daina aiki.
Sai dai yana huskantar matsin lamba daga bangarorin duka biyu, ciki har da shugabannin kasashen Turai da suke so Amurka taci gaba da aiki da yarjejeniyar, , a daya bangaren kuma Isra’ila wacce ta zargi Iran da yin karya zamba ko keta yarjejeniyar.
Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson, ya zo nan Washington jiya Litinin da zummar kama kafa manyan jami’an gwamnatin Trump domin Amurka ta ci gaba da zama a cikin yarjejeniyar. Boris ya gana da takwarar aikinsa na Amurka Mike Pompeo, kana kuma zai gana da mataimakin shugaban Amurkasa Mike Pence, da mai bada shawara a kan tsaron kasa John Bolton.
Facebook Forum