Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Amurka Ta Yi Zazzafar Muhawara Akan Janyewa Daga Yarjejeniyar Nukiliyar Iran


Paul Ryan, shugaban majalisar wakilan Amurka
Paul Ryan, shugaban majalisar wakilan Amurka

Shawarar janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka cimma da shugaba Trump ya yi ta jawo zazzafan muhawara a majalisar wakilan kasar tsakanin 'yan Democrats da Republican

Shawarar da shugaban Amurka Donald Trump ya yanke ta janye kasar daga matsayar da aka cimma da Iran kan shirinta na mallakar makamashin nukiliya, ya sake farfado da zazzafar muhawarar da aka yi a majalisar dokokin Amurka a tsakanin wakilai daga manyan jam’iyyun kasar, matsayar da suka amince da ita shekaru biyu da rabi da suka gabata.

‘Yan jam’iyyar Democrat, sun ce matakin janye Amurka daga wannan yarjejeniya, shi ne mafarin da zai sa a maida Amurkan saniyar ware a diplomasiyar Duniya, yayin da su kuma ‘yan Republican suke cewa, lokaci ya yi da ya kamata a fice daga wannan yarjejeniya, wacce za ta kawo karshen daya daga cikin nasarorin da tsohon shugaba Barack Obama ya samu a lokacin mulkinsa.

Kakakin majalisar wakilai, Paul Ryan ya ce wannan matsaya da aka cimma da Iran a lokacin mulkin Obama, na kunshe da kurakurai, kuma kasar ta Iran tana ta karya ka’idojin da aka gindaya mata tun a lokacin da aka cimma matsayar.

Sai dai, shugabar ‘yan Democrat a majalisar ta wakilai, Nancy Pelosi, ta ce, wannan gurguwar shawara da shugaban ya yanke, za ta sa a mayar da Amurka saniyar ware, ba kasar ta Iran ba. ‘Yan jam’iyyar ta Democreat sun kuma zargi Shugaban da haifar da rudani ta hanyar kaucewa gaskiyar da ke nuna cewa wannan yarjejeniya da aka kulla na tasiri ta hanyar dakile ayyukan yunkurin kera makamin nukiliyan da Iran ke yi.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG