Sabika Sheikh tana niyar komawa gida Pakistan domin bukin karamar salla, hutun kwanaki uku na karshen watan azumin Ramadan, bisa ga cewar wata kungiyar ‘yan asalin kasar Pakistan dake zaune a birnin Housten a shafinsu na Facebook.
Sabikaa ‘yar shekaru goma sha bakwai tana da kanne mata uku, suna da zama a Karachi, bisa ga rahoton tashar talabijin ta Geo a Pakistan.
Tazo Amurka ne karkashin wani shirin ilimi na musayar dalibai matasa da amurka ke gudanarwa da ake kira YES, tun ranar ishirin da daya ga watan Agusta shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai. Dama zata koma kasarta a karshen wata lokacin da shirin ke karewa.
Sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka Mike Ponpeo ya bayyana ta’aziyarsa ga dangin Sabika.
Akwai kimanin daliban kasar Pakistan dubu bakwai da goma sha biyar a makarantun sakandare da kuma na gaba da sakandare a Amurka tsakanin shekara ta dubu biyu da goma sha shida zuwa da goma sha bakwai, Karin kashi goma sha hudu cikin dari daga shekarar da ta gabata, bisa ga bayanan cibiyar gudanar da harkokin ilimin kasa da kasa.