Dubun dubatan dalibai a duk fadin kasar Amurka, da dama suna ta cewa- Ya isa haka”-sun fice daga makarantunsu jiya laraba domin zanga zangar nuna bacin ransu da yadda majalisa ta gaza daukar matakan kai tsaye, na shawo kan hare haren da ake kaiwa da bindiga.
An fara zanga zangar ne da karfe goma na safe agogon yankunan kasar, a makarantu kimanin dubu uku. Galibi an gudanar da zanga zangar ne na tsawon mintoci goma, na karrama kowanne mutum guda da aka kashe a makarantar sakandare ta Dauglas a Parkland, jihar Florida, wata guda da ya shige.
Wadansu dalibai sun rike kwalaye dake dauke da rubutu cewa, ‘jininmu yana hannuwanku” suka kuma yi allahwadai da kungiyar masu sayar da makamai ta Amurka.
Wadansu daliban sun bayyana fargaban cewa, mai yiwuwa suna cikin wadanda zasu rasa rayukansu a harin kai mai uwa da wabi da za a kai kan wata makaranta nan gaba, suka kuma shaidawa manema labarai cewa, abin ya ishe su.
An kuma yi zanga zanga a majalisar dokokin kasa ta Amurka, inda shugabar marasa rinjaye a majalisar wakilai Nancy Pelosi ta tarbi masu zanga zangar, a fadar White house kuma, daliban sun juyawa fadar shugaban kasar baya shiru. Shugaba Donald Trump baya gida a lokacin.
Malamai da dama, da iyayen daliban da jami’an gudanar da harkokin ilimi sun shiga sahun masu zanga zangar. Sai dai jami’an makaranta sun gargadi dalibai da cewa, za a iya dakatar dasu daga makaranta domin barin azuzuwansu ba tare da izini ba.
Facebook Forum