'Yanbindigan suna kai hare-hare ne akan jami'an tsaro. Kasa da mako guda 'yanbindigan sun hallaka jami'an tsaro guda bakwai da suka hada da sojoji da 'yansanda.
Hari na farko shi ne wanda 'yanbindigan suka kaddamar a wurin duba motoci dake Toro inda suka kashe jami'an tsaro guda uku. Hari na biyu kuma sun kai ne a unguwar Wuntin Dada nan ma sun kashe soja guda daya suka kuma raunata guda uku. Su ma 'yanbindigan an kashe daya daga cikinsu. Hari na uku shi ne wanda suka kai akan kamfanin Shiyei a daren Litinin. Kamfanin mallakar 'yan kasar Sin ko China ne. A wannan harin sun hallaka 'yansanda guda biyu.
Wani ma'aikacin kamfanin ya yi bayani inda yace wasu ne da ba'a san ko su wanene ba suka farma kamfanin suka kuma kashe 'yansanda biyu. Kawo yanzu dai ba'a kama kowa ba. An watse a kamfanin domin kowa yana ta kansa ne.
Tun farko al'ummar wurin sun ki jinin kamfanin gaba daya wanda yana tonar ma'adanan kasa ne. Mutanen wurin suna korafi da aikin 'yan Sin din. Sun ce suna bata masu ruwan da dabbinsu ke sha da nasu ayyukan. Wannan lamarin kuma yasa su 'yan kasar Sin din suna kwashe kayansu da nufin barin kasar.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.
Your browser doesn’t support HTML5