Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Rikici ya Barke a Garin Wukari


Sabon rikici a Wukari.
Sabon rikici a Wukari.

Ana Cikin Zaman dar-dar a Wukari Biyo Bayan Sabon Rikici

Alumomin yankin Wukari dake kudancin jihar Taraba, na cikin zaman dar-dar biyo bayan wani sabon rikici da ya sake barkewa a garin Wukari a yau talata.

An kona gidaje da dama da kuma hasaran dukiyoyi masu dubin yawa, kawo yanzu ba’a san addadin yawan mutanen da suka mutu ba.

Dama an dade ana zaman doya da manja tsakanin alumomin yankin, kuma wannan rikicin ya barke ne kasa da awowi ashirin da hudu bayan wani taron sulhu da akayi a tsakanin bangarorin Jukunawa da Hausawa da Fulani dake garin.

Wasu da suka tsira da rayukansu, sun ce da sayin safiya ne aka barke da jin harbe-harbe da kuma kone-kone.

Kakakin rudunar ‘yan sandan jihar ta Taraba, ASP James Kwaji yace an tura Karin jami’an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da doka da oda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG