‘Yan wasan Brazil Da Suka Makale A Ukraine Sun Nemi A Kai Musu Dauki

Dan wasan PSG/ Brazil, Neymar

Dan wasan PSG Neymar ya ce yana taya 'yan kasar tasa da addu'ar samun mafita yayin da suke cikin wannan hali.

Wasu ‘yan wasan Brazil da ke kwallo a wasu gaggan kungiyoyin kwallon kafa biyu a Ukraine sun yi kira ga gwamnatinsu da ta kai musu dauki, saboda mamayar da Rasha ta kai kasar ta rutsa da su.

Wata tawagar ‘yan wasa daga kungiyar Shakhtar Donetsk da Dynamo Kyiv, sun wallafa wani bidiyo a shafukan sada zumunta tare da iyalansu, inda aka gansu a wani otel suna kira ga hukumomin kasarsu ta Brazil da su kai musu dauki.

Bidiyon ya hada har da dan wasan kasar Uruguay Carlos de Pena da ke taka leda a Dynamo kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

A cewar ‘yan wasan, an rufe kan iyakokin kasar kuma man fetur ya katse.

“Mun zaku matuka. Muna shiga cikin yanayi na tsaka mai wuya, “dan wasan Shakhtar mai tsaron baya Marlon Santos ya rubuta a shafinsa na Instagram

“Muna samun tallafi daga kungiyarmu, amma tarabbabin da muka shiga ya yi yawa.” Santos ya kara da cewa.

Dan wasan Brazil da ke buga kwallo a Paris Saint Germain, Neymar ya wallafa bidiyon a shafinsa na Instagram, inda ya ce yana taya ‘yan wasan kasar tasa da addu’a.

A ranar Alhamis dakarun Rasha suka mamaye wasu biranen Ukraine, ciki har da Kyiv babban birnin kasar.