Dan wasan Brazil Neymar ya taya takwaran karawarsa na Argentina, Lionel Messi murnar nasarar da suka samu ta lashe kofin gasar Copa America.
Bayan sama da minti 90 suka kwashe suna fafatawa a matsayin abokanan hamayya a filin wasan, ‘yan kwallon biyu, wadanda sun taba buga wasa tare a Barcelona, sun rungumi juna, inda Neymar ya taya Messi murnar nasarar da suka samu.
Rungumar junar da suka yi, ta dan dauki tsawon lokaci, abin da ya ja hankalin masu sharhi da masoya wasan kwallon kafa a duniya, ya kuma nuna kyakkyawar alaka da ke tsakanin fitattun 'yan wasan na duniya.
Argentina ta doke Brazil da ci 1-0 a wasan, wanda aka buga a filin wasa na Maracana da ke Rio de Janeiro a ranar Asabar.
Wannan shi ne kofi na farko da Argentina ta ci cikin shekara 28, kuma ita ce nasara ta farko da Messi ya samu ta daga babban kofi karkashin kungiyarsa ta Argentina.
Rabon da ta dauki kofin wata babbar gasa tun a shekarar 1993.
Angel Di Maria ne ya ci wa Argentina kwallon da ta ba su nasara a minti na 22.