Dan wasan Paris Saint Germain Neymar, ya sabunta kwangilarsa da kungiyar har zuwa 2025, kamfanin dillancin labaran AP ya ruwaito.
Wannan labari ya kawar da duk ka-ce-na-ce da ake ta yi kan cewa zai bar PSG a karshen wannan kakar wasa a matsayin dan wasan mai zaman kansa.
A ranar Asabar PSG ta sanar da sabunta kwantiragin, inda ta wallafa wani bidiyonsa yana sanye da wata rigar kwallo da aka rubuta 2025 a baya.
Rigar har ila yau tana dauke da rubutun “Ici c’est Paris” da harshen Faransanci, wato “Nan ne Paris”, wanda shi ne sannan taken masoyan kungiyar.
Dan shekara 29, kwangilar Neymar a PSG za ta kare ne a watan Yuni, tare da dan wasa Kylian Mbape - wanda har yanzu bai sabunta kwangilarsa da kungiyar ba.
Ana dai danganta Mbape da komawa Real Madrid a kasar Spaniya.
Neymar ya zura kwallo 85 a wasa 112 tun da ya koma PSG daga Barcelona, inda aka biya zunzurutun kudi euro miliyan 222 a tsawon shekara hudu da zai kwashe a kungiyar.
An dakko shi ne tare da Mbape, wanda aka siyo akan euro miliyan 180 daga Monaco.