Lionel Messi ya samu gudunmowa sau uku a cin 3-1 a nasarar da su ka yi kan kulub din 10-man Saint-Etienne ranar Lahadi don taimaka ma kulub din Paris Saint-German (PSG) wajen fadada fintinkau da ya yi har zuwa maki 12 a gasar lig ta Faransa, to amma raunin da fitaccen dan wasan tsakiya, Neymar ya ji ya kawo cikas ga wannan nasarar.
Za a daina ganin majagaban Kulub din na Paris Saint-German har na tsawon makwanni 8 saboda wannan rauni da ya ji a kafar hagu. Sai da aka ciccibi Neyman yayin gasar ta lig din Faransa a Saint Etienne, inda su ka yi nasarar cin 3-1 a ranar Lahadi. Haka zalika tantanin kafarsa sun tsage, a cewar PSG a wata takardar bayani ranar Litini. An ciccibi dan wasan gaban, wanda dan asalin kasar Brazil ne, a minti na 87 da fara wasa bayan da ya gurde kafarsa ta hagu lokacin da ya fuskanci turjiya daga Yvann Macon.
Wannan shi ne na baya a jerin raunukan da fitaccen dan wasan na PSG ya yi ta samu. Ko a watan Disamban bara ma sai da aka kinkimi Neymar saboda rauni a kafar ta dama. Tun bayan da din PSG ta saye shi kan kudi mafi yawa a tarihin kwallo, wato euro milliyan 222 (dala miliyan 250), ya kuma samu raunuka a girji, wajejen maraya, da jijiya, baya kuma ga karyewar da ya yi a tafin kafar dama a watan Fabrairun 2018.
“Mu murmure aga wannan,” a cewar Neymar a shafinsa na Instagram. Ya kara da cewa, “Abin takaici wannan cikas din na daya daga irin kalubalen da dan wasan matso jiki ke samu. Abin da ya faru, ya faru; bari mu daga kai gabanmu kadi, kuma mu dage! Zan dawo da kuzari fiye da haka.”
Kungiyar Saint-Etienne ta share fagen cin kwallon ne minti na 23 da fara wasan, wanda aka yi a yanayi mai dusar kankara. Wahbi Khazri ya tinkari Timothee Kolodziejczak, wanda Gianluigi Donnarumma ya kama kwallon da ya bugo. To amma kwallo ta yi dira ta biyu ne gaban Denis Bouanga, wanda ya lailaye mai tsaron gidan Italy.
Mai tsaron gida na Ingila, Etienne Green ya jinkirta yinkurin PSG na sake shan gaba ta wajen kawar da kwallon da Neyman ya bugo a karkace a minti na 40 da kuma rashin katabus din da Mbappe ya nuna a minti na 41.
To amma famar da Saint-Etienne ke yi ta dada zama da wahala a cikin rabin lokaci bayan da aka tura Kolodziejczak taka burki ma Mbappe, wanda kan biyo kwallo daga from Angel di Maria. Dan wasan Brazil, Marquinhos ya rama cin da aka masu bayan da ya tura kai ya saita kwallon da Messi ya cillo.
Duk da fin yawan ‘yan wasa, PSG ta yi ta fama wajen kokarin yin nasara. Green ya taka ma Neymar burki a mint ana 69 kuma Messi ya kasa cin kwallon da ta dira karo na biyu gabansa.
Daga bisani dai PSG ta sha gaba a minti na 79 bayan da Messi ya samu Di Maria, wanda ya labe a kwanar karshe can. A dab da cikar lokaci, Messi ya tura kwallo ma Marquinhos, wanda ya yi tsalle sama ya zarce Miguel Trauco, ya daki kwallo da ka.
“Ina mai matukar farinciki da gamsuwa,” abin da Sergio Ramos ya fada kenan a shafin yanar gizo na kulub din. Ya kara da cewa, “Wannan rana ce ta musamman a gare ni, bayan da na dau lokaci mai yawan gaske ba tare da buga wasa ba. Ya kasance da muhimmanci a gare ni da na taimaka ma kulub din, na kasance tare da ‘yan wasan, kuma ya kasance na yi wasa har na tsawon minti 90.”