'Yan Tawaye Sun Yarda da Shirin Tsagaita Wuta a Sudan ta Kudu?

Sojojin Sudan ta kudu cikin mota a garin Bor, da gwamnati ta kwace daga hanun 'yan tawaye cikinmakon jiya.

A kokarin shawo kan 'yan tawaye a Sudan ta kudu, gwamnatin kasar ta amince zata saki wasu daga cikin mutane 11 da take tsare da su kan zargin shirya mata jutyin mulki.
Yayinda hukumomin kasa da kasa suke matsa kaimin ganin an cimma tsagaiata wuta a rikicin da ake yi a Sudan ta kudu, rundunar mayakan kasar tace dubban matasa dauke da makamai wadanda suke biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar sun doshi garin Bor dake hanun gwamnati.

Kakakin runduar sojojin Sudan ta kudu Phillip Aguer ya gayawa MA jiya Asabar cewa, mayakan da suke goyon bayan macher da ake yiwa lakabin “fararen soja” suna shirin kai hari kan garin dake tsakiyar kasar ne, da sojojin gwamnati suka sake kwacewa a farkon makon jiya.su ma matasan kamar tsohon mataimakin shugaban kasar ‘yan kabilar Nuer ne, yayinda shugaba Silva Kiir dan kabilar Dinka ne.

Duk da haka, kakakin sojan kasar Sudan ta kudun yace dakarun kasar da suke Bor zasu iya maganain duk wani irin farmaki da aka kai kan garin.

Fadan wanda ya dauki sigar kabilanci ya barke ne a farkon wannan wata lokacinda shugaban kasar ya zargi tsohon mataimakinsa Macher da kitsa yi masa yujin mulki.
MDD tace fadan ya hallaka fiye da mutane dubub daya, ya kuma raba dubbai da muhallansu.

A kokarin kawo karshen rikicin na tsawon mako biyu, kungiyar shugabannin kasashe dake gabashin Afirka sun bada sanarwa ranar jumma’a cewa gwamnatin Sudan ta kudu ta amince da “shirin tsagaita wuta”, da kuma fara shawarwarin wanzarda zaman lafiya. Haka nan kuma suka ce gwamnatin ta amince zata saki 8 daga cikin fursinonin siyasa 11 da ake zarginsu da kitsa juyin mulkin.

Amma jiya Asabar wata mai goyon bayan Macher, Rebecca Nyandeng ta fadawa MA cewa dakarun Machaer ba zasu amince da duk wani shirin tsagaiata wuta ba har sai gwamnati ta saki fursinonin su duka 11.

A nasa bangaren saura kiris, Macher ya fito fili ya amince da kiran da gwamnati take yin a tsagaiata wuta. Ya gayawa gidan rediyon BBC cewa, tilas ne da farko a kafa hanyoyin sa ido kan duk wata yarjejeniyar da aka kulla tukun.