Tun daga 1960 da kasar tayi bikin samn ‘yancin kanta daga hannun ‘yan mulkin mallaka, zuwa juyin mulkin da soja suka rika yi babu kakkautawa, Nigeria sai ta kasance wata tauraruwar kasa a nahiyar Afirka wadda kasa da kasa suka rika yin watsi da ita, im banda ‘yan mulkin mallakar Faransa, da dillalan Lu’u-Lu’u (Diamond) da manyan ‘yan farauta namun daji sai kuma manyan kungiyoyin ‘yan tawayen dake mamaye da kan iyakokinta.
Michel Djotodia, jagoran mayakan ‘yan tawaye ne wanda a karshen mako ya ayyana kansa shugaban kasa bayan da sojin da yake yiwa jagoranci suka sami nasarar mamaye babban birnin jumhuriyar Afirka ta tsakiya, sannan ya tara manyan sojin Gwamnatin kasar a Bangui babban birnin kasar a ran 28 da watan Maris shekara ta 2013. A dai-dai lokacin ne kuma, shugaba Michel Djotodia ya juya ga mayakan ‘yan tawayen Musulmi, cikinsu harda sojin haya daga kasashen Chadi da Sudan, sai kuma ‘yan barandar dake kiran kansu mayakan “Seleke”, ko ‘yan hadin gwiwa domin su taimaka masa kwace ragamar mulki watanni takwas da suka gabata. Kamar yadda aka ji daga bakin Ministan shari’ar jumhuriyar Afirka ta tsakiya,Arcene Sende ne cewa, an kuma sami hadin gwiwar Fursunoni dubu da dari biyar “1,500” da Sulusinsu an yanke masu hukuncin kisa ne a dalilin kisan da suka yi duk suka fada rundunar sojin Afirka ta tsakiya.