A jiya jumma’a ne Ofishin MDD a Sudan ta kudun ya bada sabon adadin kasa da abunda jami’an majalisar dake New York suka bayyana cewa, an kashe farar hula 20 lokacinda aka kai hari a Akobo. Jiragen masu saukar ungulu na majalisar sun tafi garin jiya domin su kwashe wadanda suka tsira daga harin, kuma sa kara nazarin halinda ake ciki.
Ofishin majalisar yace tarzomar ta barke ne bayanda mataasa su kamar dubu biyu ‘yan kabilar Nuers suka yiwa sansanin zobe daga nan kuma sai suka bude wuta.Majalisar tace matasan sun auna harin ne kan ‘yan kabilar Dinka da suke mafaka a sansanin. Sojojin kiyaye zaman lafiya suka ce sunyi kokarin tattaunawa da maharani, amma sai su fuskanci luguden wuta babu kakkautawa.
Jakadiyar MDD ta musamman a Sudan ta kudu Hilde Johnson tace abunda ya faru a Akobo laifi ne kuma tilas a hukunta wadanda suka kai harin.
Ana kiyasin kimanin farar hula dubu 35 ne suka zaman mafaka a sansanonin mDD a Sudan ta kudu tun lokacinda rikici ya barke a kasar cikin makon nan.
Shugaban kwamitin sulhu na MDD Gerard Araud ya fada jiya jumma’a cewa wasu matasa dauke da makamai sun tattaru a harabar sansnain MDD a garin da ake kira Bor, inda kimanin farar hula dubu 14 suke zaman mafaka.