Kungiyar nan mai lakabin IGAD ce ta bada snarwar haka bayan ta kammala wani taron koli da ta kira a birnin Nairobi jiya jumma’a. Kungiyar tayi kira ga magoya bayan shugaba Silva Kirr, da mgoaya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, suma su ayyana wannan mataki.
Machar bai halarci taron ba, kuma bai bada wata sanarwa nan da nan ta maida martani kan wannan kira da taron kolin yayi ba.
Ahalinda ake ciki kuma ayarin farko na karin sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD sun isa Sudan ta kudu a jiya jumma’a. MDD tace karin jami’an tsaro 72 ‘Yansanda daga kasar Bangladesh sun isa kasar daga jamhuriyar demokuradiyyar kwango. A makon jiya ne kwamitin sulhu na MDD ya amince da kara sojojinta a Sudan ta kudu na wucin gadi zuwa dubu 14, daga dubu takwas ahalin yanzu.
A wani lamari na daban a Sudan ta kudu din wani dan jarida a Sudan ta kudu ya bayyana irin mummunar tarzomar da tilas ta masa da iyalinsa gudu zuwa cikin daji.
Da yake magana d a sashen turanci na MA mai yada shirye shiryensa zuwa ga nahiyar Afirka, David Mayar ya fada jiya jumma’a cewa sojoji sun harbe shi ranar Alhamis yayinda shi da iyalinsa suke kokarin komawa garinsu Bor.
Mayar yace bisa kuskure sojojin gwamnati wadanda suke da alamun maye suka harbe shi.
Mayer ya sami jinya daga raunind a ya samu a wani sansanin MDD dake garin na Bor.