‘Yan Sandan Pakistan Sun Kama Masu Zanga-zanga Da Dama A Karachi

'Yan sanda A Karachi Sun Kai Hari Kan Masu Zanga-zanga

Jam’iyyar ta ce daya daga cikin mambobinta ya mutu a rikicin.

‘Yan sanda a kasar Pakista sun harba hayaki mai sa hawaye tare da amfani da kulake a kan dubban masu zanga-zanga ranar Lahadi a birnin Karachi bayan masu zanga-zangar sun karya shingen jami’an tsaro.

Magoya bayan jam’iyyar masu ra’ayin rikau ta Islamist kusan 2,000 ne suka yi kokarin isa gidan jaridar birnin don nuna adawa da wata zanga-zangar da kungiyoyin farar hula suka yi game da kisan wani da ake zargi da aikata sabo a lokacin da yake tsare.

Magoya bayan jam’iyyar Tehreek-e-Lababaika Pakistan wato TLP sun yi ta jifa da duwatsu kan jami’ai tare da kona wata motar sintiri a lokacin da ‘yan sanda suka hana su isa gidan manema labarai.

Jam’iyyar ta ce daya daga cikin mambobinta ya mutu a rikicin. ‘Yan sanda sun kama mutane kusan 20 daga cikin zanga-zangar biyu.

Ministan Harkokin Cikin Gida na Yankin Zia Ul Hassan ya ce hukumomi na fargabar barkewar rikicin saboda jam’iyun siyasar biyu da kungiyoyin fararen hula sun yi kira da a gudanar da zanga-zanga a ranar guda.