An shiga rana ta uku a wasu biranen Najeriya ana gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa, yunwa da sauran matsaloli da ke addabar al’ummar kasar.
Wasu rahotanni na nuni da cewa rundunar ‘yan sandan jihohin Bauchi da Gombe sun kama matasa masu zanga-zangar su fiye da dari (100), bisa zarginsu da aikata laifuka daban daban yayin zanga-zangar da aka fara a ranar Alhamis.
A hirarsa da Muryar Amurka ta wayar tarho, kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi CP Auwal Musa, ya ce suna ci gaba da yin sintiri na tabbatar da cewa komai na zaune lafiya.
CP Auwal ya ce a cikin artabun da su ka yi da masu zanga-zangar sun kama kusan mutane sittin da su ka hada da matasa, yara kanan da mata.
“Muna tuhumar su da aikata laifuka da suka hada da tada hankali da jiwa jama’a ko jami’ai rauni ko lalata dukiya,” in ji CP Auwal.
A daya gefen kuma a jihar Gombe makwabciyar jihar Bauchi, kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Gombe, Buhari Abdullahi, ya ce wasu matasa sun zo sun yi yunkurin shiga cikin gidan gwamnatin jihar Gombe kuma suka fara jifa da barnata kayan gwamnati da shagunan mutane da ke kusa, har da wani otel da su ka fara lalatawa.
Ya ce jami’an ‘yan sandan ba su da zabi illa su dauki mataki, inda su ka fara harba barkonon tsohuwa domin tabbatar da an gujewa lalacewar doka da orda.
Ya kara da cewa hukumar ta ci gaba da yin sintiri a dukkan fadin jihar, domin tabbatar da cewa ta kwato kayan da aka sacewa mutane kuma an yi nasara kwato kayan da dama, sannan sun kama mutane 69.
Sai dai kungiyar kare hakkin dan Adam ta Civil Liberty Organization, da ke jagorantar zanga-zangar, a cewar Shugaban Kungiyar Shiyyar Arewa Maso Gabas, Muhammad Aliyu Wayas, barayi ne su ka aikata ta’asar ba masu zanga-zanga ba ne.
Wani dan rajin kare hakkin dan adam, Barista Abdullahi Usman Toro, ya ce masu rike da madafun iko ba su dauki talakawa a bakin komai ba, kuma abun da ya faru ishara ce ga shugabanni.
Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad:
Your browser doesn’t support HTML5