Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Salwantar Rayuka Na Karuwa A Najeriya Sakamakon Tabarbarewar Tsaro Da Zanga-zanga


Wasu masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya
Wasu masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

Matsalar rashin tsaro wadda tana daya daga cikin abubuwan da suka tunzura 'yan Najeriya su fito yin zanga zanga na ci gaba da daukar rayukan jama'a musamman a arewacin kasar.

Wannan na zuwa ne lokacin da 'yan ta'adda suka hallaka mutane goma sha uku ciki har da jami'an tsaron al'umma biyar a Sakkwato, a wasu hare hare biyu da suka kai cikin kwana uku.

Daga cikin matsalolin da 'yan Najeriya ke yi wa zanga zanga akwai matsalar rashin tsaro wadda ta jima tana addabar jama'a kuma ta yi sanadin salwantar rayuka da dukiyoyi, kuma kokarin da mahukunta ke yi ya kasa dakile matsalar.

Wani abu da ke tabbatar da ci gaba da wanzuwar matsalar shi ne wasu hare-hare da 'yan bindiga suka kai a karamar hukumar Gudu ta jihar Sakkwato, yankin da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar, inda suka hallaka mutane da dama.

Kantoman karamar hukumar Umma Maikano ya ce 'yan bindigar sun kai harin ne ranar Asabar da ta gabata suka harbe manoma shida, inda biyar suka mutu, kuma kwana biyu bayan wannan harin suka dawo suka yi wa jami'an tsaron al'umma kwanton bauna suka kashe mutane takwas hadi da jami'an su biyar.

Wannan zanga zangar dai da ta shigo kwana na biyu yau ita ma ta zama sanadin salwantar rayukan wasu jama'a a wasu jihohin Najeriya kamar yadda wasu bayanai da ma hotuna suka nuna a shafukan sada zumunta na yanar gizo.

A jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya ma bayanai sun nuna a garin Yauri jami'an tsaro na'yan sanda sun yi harbi akan masu zanga zangar har an samu salwantar rayuwa, da kuma raunuka.

Muryar Amurka ta yi kokarin jin tabakin rundunar 'yan sanda ta jihar Kebbi a kan wannan batun na harbi lokacin zanga zanga amma kakakin bai dauki kiran ba.

Duk da yake yau ne rana ta biyu ta zanga zanga, jama'a basu fito ba a jihar Sakkwato inda a Kebbi an samu fitowar jama'a a Birnin Kebbi sai dai ba kamar rana ta farko ba, kuma duk da haka al'amurra sun soma daidaita, inda masu shaguna sun soma buda wuraren sana'ar su kuma jama'a na ci gaba da lamurran su cikin lumana, amma duk da haka jami'an tsaro na ci gaba da sintiri a manyan tituna.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammadu Nasir:

Salwantar Rayuka Na Karuwa A Najeriya Sakamakon Tabarbarewar Tsaro Da Zanga-zanga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG