Zanga-zangar na ci gaba ne dai duk da cewa shugaban kasar ya janye kudirin karin harajin.
Adadin mutanen da suka fito yin zanga-zangar ya ragu sosai idan aka kwatanta da yawan mutanen da suka fito a baya-baya nan. Shugaba William Ruto ya janye dokar ne a ranar Larabar da ta gabata, kwana guda bayan arangamar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 23, inda kuma aka kai wa majalisar dokokin kasar hari na ‘dan gajeren lokaci tare da cinna wuta.
Ruto dai na fama ne da rikici mafi muni da bai taba gani ba a shugabancinsa na tsawon shekaru biyu a daidai lokacin da kungiyar masu zanga-zangar da matasa ke jagoranta ke karuwa cikin sauri sunna Allah wadai da karin harajin da aka yi a yanar gizo zuwa gangamin neman sauyi na siyasa.
Sakamakon rashin tsarin shugabanci na gari, masu zanga-zangar sun rabu kan yadda za a gudanar da zanga-zangar.
"Kada mu zama masu wauta yayin da muke fafutukar samar da ingantacciyar kasar Kenya," in ji Boniface Mwangi, wani fitaccen mai fafutukar tabbatar da adalci, a wani sakon da ya wallafa a shafin Instagram.
Ya bayyana goyon bayansa ga zanga-zangar a ranar Alhamis amma ya nuna adawa da kiraye-kirayen kutsawa kan gidan gwamnati, da ofisoshin shugaban kasa da kuma gidansa, matakin da ya ce zai iya haifar da mummunan tashin hankali da kuma amfani da hakan wajen ganin an murkushe su.
A Nairobi babban birnin kasar dai, 'yan sanda da sojoji sun yi sintiri a kan tituna ranar Alhamis tare da toshe hanyar shiga fadar gwamnati. 'Yan sanda sun kuma harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa mutane goma sha biyu da suka taru a tsakiyar birnin.
-Reuters