A ranar Talata yan sandan Kenya suka isa babban birnin Haiti, Port-au-Prince, domin wanzar da wani kudurin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya domin magance tashe tashen hankullan 'yan kungiyar daba.
A watan Yulin da ya wuce ne kasar Kenya ta amince ta shugabancin wata rundunar kasa da kasa domin magance tashe tashen hankali a kasar ta Haiti, inda kungiyoyin 'yan daba ke iko da mafi yawan birnin, da kashe kashe, satar mutane da cin zarafi ta lalata, da su ka zama ruwan dare a kasar.
Shugaban Amurka Joe Biden ya fada cikin wata sanarwa cewa, al’ummar Haiti sun cancanci zama lafiya a gidajen su, su gina ingantacciyar rayuwa ga iyalan su, su kuma more 'yancin demokradiyya. Yace, makomar Haiti ta dogara ne kan komawa ga gwamnatin demokradiyya. Biden ya kara da cewa, duk da dai ba lallai ba ne haka ta cimma ruwa a dare daya, kudurin ya samar da ingantacciyar kafar da za a cimma wannan gurin.
Mutane sama da dubu dari biyar da tamanin ne su ka rasa muhallan su a sassan kasar sakamakon gungiyoyin daba. Tun gabanin isar dakarun na Kenya a kasar, mai magana da yawun ma’aikatar cikin gida na Amurka Matthew Miller, ya bayyana fatan ganin samun cigaba a bangaren tsaro, musamman a kan abinda ya shafi samun tallafin jinkai da hada hadar harkokin tattalin arziki.
Kungiyoyin 'yan daba sun rika shiryawa da kai hare hare kan gine ginen gwamnati, domin ganin tsohon Firaiministan kasar Ariel Henry bai komo cikin kasar ba. Kungiyoyin 'yan daban ke iko da ofisoshin Yan sanda sama da dozin guda, da harbe harben bindiga a babban filin jirgin saman kasar, da sakin sama da daurarru dubu hudu(4,000) da ga gidan kaso biyu mafiya girma a kasar.
Dandalin Mu Tattauna