Janye kudirin ya biyo bayan suka daga kungiyoyin kare hakkin jama'a da 'yan kasar da ke ikirarin cewa zai baiwa gwamnati damar murkushe 'yan adawa.
Kakakin Majalisar dokokin Najeriya kuma mai daukar nauyin kudirin, Tajudeen Abbas, ya janye kudurin dokar a wata sanarwa a ranar Laraba.
Abbas ya ce an dauki matakin ne saboda damuwar da jama’a suka nuna da kuma yin la’akari da yanayin da Najeriya ke ciki a halin yanzu.
Idan an tabbatar da wannan kudiri ta zama doka, ‘yan Najeriya na iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari ko wata babbar tara ga dan kasar da bai karanta taken kasa ba, da kuma hukuncin daurin shekaru biyar ga masu tare hanya ba bisa ka’ida ba, da kafa da dokar hana fita ba bisa ka'ida ba ko gudanar da tattaki ba bisa ka'ida ba.
Masu sukar mataki kamar su Damilare Akinola dan rajin hakkin bil Adama a Abuja sun ce wani yunkuri ne hukumomi ke yin a hana fadar albarkacin baki
Ya ce “Karfin jama’a ya danne nasu, shi ya sa kake ganin an janye kudirin da ba a yi zurfin tunani ba akai. Ko kafin a fara gabatar da kudirin, an tauye hakkin jin ta bakin jama’ar Najeriya. Wannan wani yunkuri ne na kara wa hukuma karfi. Don haka, wannan yunkurin ne bai zo da mamaki ba."
Kudirin ya tanadi duk wani dan kasa da ya bijire wa hukuma ka iya fuskantar hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari.
An gabatar da kudirin ne yayin ake zanga zangar kin jinin gwamnatin a Najeriya.
Tun da farkon wannan wata, dubban mutane sun yi tattaki a kan titunan manyan biranen Najeriya, suna kira ga gwamnatin ta janye sauye-sauye da ta yi musamman janye tallafin man fetur.
Sai dai zanga zangar ta koma tashin hankali yayin da jami’an tsaro suka yi amfani da karfin tuwo wurin tarwatsa masu zanga zangar. Kungiyar rajin hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce mutane 23 ne aka kashe.