Shugaban hukumar tattarawa da kayyade kudade ta Najeriya RMAFC Mohammed Bello Shehu ya ce bayanan da suka fito daga bakin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan batun albashin ‘yan majalisa abin dubawa ne, domin akwai tanade tanade da Kundin Tsarin Mulki yayi kuma ana bin su daki daki.. Shehu ya baiyana haka ne a lokacin da ya gana da manema labarai a Abuja,a ciki har da wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda. Ga rahoton da ta hada mana.
Bayanan da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi cewa rashin da'a ne yadda ‘yan majalisar majalisar dokokin kasar suke yanke wa kansu albashi da alawus alawus, na ci gaba da ta da kura musamman a kafofin yada labarai da dandalin sada zumunta.
Wannan ya kai ga ‘yan majalisar dokin na tarayya mayar da martani a wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin ajalisar dattawa Yemi Adaramodu, da takwaransa na majlisar wakilai Akin Rotimi.
Sanarwar ta ce “majalisar dokokin kasar ta 10 ta sha bamban da ta zamanin Obasanjo.”
A na shi martanin, dan majalisar dattawa daga jihar Nasarawa ta Yamma Ahmed Aliyu Wadada, ya ce yana girmama Obasanjo, amma ya lura Obasanjo na amfani da abubuwan da suka faru a baya wajen yanke hukunci kan lokacin da ake ciki a yanzu, kuma a cewar sa, yin haka ba daidai bane.
Wadada ya ce majalisar ba ta taba sauya komi ba tun daga 1999 kawo yanzu, yana mai cewa “kuma Obasanjo ya shugabanci kasan nan daga 1999 zuwa 2007, idan haka ne, me ya sa bai dauki mataki ba?”
Dan majalisar dattawan ya yi kira ga tsohon shugaban kasa Obasanjo da ya kara duba maganganun sa sosai, domin “babu wanda ke kayyade wa ‘yan majalisar dokoki da manyan ma'aikatan gwamnati da ma shugaban kasa albashi sai hukumar tattara kudade da kaiyade su wato RMAFC.
To sai dai a na ta bangare, hukumar tattara kudade da kayyade su wato RMAFC, cewa ta yi kalaman na tsohon shugaban kasa abin dubawa ne, don haka za ta bi diddigi domin binciko hakikanin gaskiya kan lamari, tare kuma da yi wa ‘yan kasa cikakken bayani.
Shugaban hukumar Mohammed Bello Shehu ya ce hukumar tana da wani kwamiti na cikin gida za zai bi diddigi da bincike kan wannan lamarin.
Shehu ya ce “idan har ‘yan majalisar suna yankawa kan su albashi daban da wanda kundin tsarin mulki ya tanada kamar yadda Obasanjo ya yi zargi, to hakan ba daidai ba ne domin hukumar tana hada wa ‘yan majalisar albashinsu har da alawus-alawus kama daga batun muhallin su, ma'aikatan su da sauran su, kuma ana hada masu kudin a lokacin biyan albashin su na wata.”
Shehu ya bayyana jadawalin albashin da doka ta kayyade wa manyan shugabannin gwamnati, inda albashin shugaban kasa hadi da alawus-alawus ya kama N1,350,000 a wata, sai albashin gwamna da alawus din sa N1,100,000, dan majalisar dattawa naira miliyan daya, yayin da dan majalisar wakilai ya ke karbar albashin kasa da naira miliyan daya.
Saurari rahoton Medina Dauda.
Dandalin Mu Tattauna