A shekara ta 2022, gwamnatin mulkin sojan da ta karbi mulki a juyin mulki a shekarar 2021 ta ba da shawarar gudanar da mulki karkashin gwamnatin rikon kwarya na tsawon shekaru biyu kafin gudanar da zabe, bayan tattaunawa da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, amma ba ta nuna alamar yunkurin shirya zabe ba.
Sabon daftarin tsarin mulkin da ake sa ran za a kada kuri'ar raba gardama da ba a yanke hukunci kai ba, zai iya ba da dama ga kasar mai arzikin tama da karafa a yammacin Afirka ta koma kan tsarin mulkin damokaradiya.
Sabon shirin da aka gabatar a ranar Litinin a zauren Majalisar rikon kwarya ta kasa, wanda ke aiki a matsayin Majalisar dokoki a karkashin mulkin wucin gadi, bai hana mambobin gwamnatin da ke mulki shiga harkokin zabe ba.
Tsohon Shugaban kasar Alpha Conde, mai shekaru 86, wanda sojoji suka hambarar da shi kusan shekaru uku da suka wuce, ba zai shiga takarar ba saboda kayyade shekarunsa.
Alpha Conde
Conde dai ya haifar da fushi da rashin kwanciyar hankali har zuwa juyin mulkin, bayan da ya sauya kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi damar sake tsayawa takara a karo na uku a shekara ta 2020, bayan hawansa mulki a shekara ta 2010.
Idan daftarin sabon kundin tsarin mulkin ya samu amincewa, za a zabi shugaban kasa na tsawon shekaru biyar wanda za a sabunta shi sau daya, wanda hakan zai rage wa'adin shugaban kasa daga shekaru shida a kundin tsarin mulkin da aka amince da shi a shekarar 2020.
Ya zuwa yanzu dai ba a san lokacin da za a gudanar da zaben shugaban kasa ba.
Dandalin Mu Tattauna