Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ku Baiwa Gwamnati Karin Lokaci Ta Biya Bukatunku - Majalisar Dattawa


Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)
Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Rokon na zuwa ne bayan da Majalisar Dattawan ta sake hallara bayan wata ganawar sirrin da ta shafe kusan sa’o’i biyu a yau Laraba.

Majalisar Dattawan Najeriya ta roki masu zanga-zanga su baiwa gwamnatin tarayya karin lokaci domin sauye-sauyen da take gabatarwa su haifar da da mai ido tare da biyan bukatunsu.

Shugaban Makalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa gwamnatin ta fara biyan bukatun masu zanga-zangar ciki har da batun mafi karancin albashi da na rancen karatu ga dalibai da sayarwa matatu da danyen mai.

Ya cigaba da cewa, a shirye majalisar take ta yi dokoki a kan batutuwan da zasu kawowa ‘yan Najeriya saukin rayuwa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG