Kawunan 'yan Najeriya sun rabu akan kalamun da Farfasa Soyinka yayi dangane da hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa akan masallatai da mijami'u.
A ra'ayin Farfasa Soyinka hare-haren ka iya zama sanadiyar hadin kan Musulmai da Kiristocin Najeriya to sai dai 'yan Najeriya sun rabu yayin da suka cigaba da bayyana ra'ayoyinsu akan furucin shi Farfasan.
Wani Muhammed Murtala yace harin da 'yan Boko Haram ke kaiwa akan masallatai da mijami'u ba zai kawo hadin kan musulmi da kirista ba domin kowa an kashe nasa. Shi ma Abdulhakim Adebayo cewa yayi hadin kai tsakanin musulmi da kirista ba zai yiwu ba domin 'yan Boko Haram ba musulmai ko kiristoci ba ne. Suna cutar Allah ne. Amma Umar Lamido ya yadda da maganar da Farfasa Soyinka yayi domin ba kabila guda ko addini guda 'yan Boko Haram suke kaiwa hari ba. Suna kaiwa musulmi da kirista da masallaci da coci hari.
Wani Abdullahi yace hare-haren da 'yan Boko Haram ke kaiwa a masallatai da mijami'u yakamata a taru a hada kai a kuma cigaba da addu'a Allah Ya kawo karshen tashin tashinar. Yakamata a duba maganar da Farfasa Soyinka yayi a hada kai tsakani da Allah a kuma cigaba da addu'a. Idan shugabannin addinan suka hada kan mabiyansu za'a samu hadin kai kamar yadda Farfasa Soyinka yayi harsashe.
A akasarin gaskiya abun da 'yan Boko Haram keyi ba addini ba ne sabili da haka yana iya kawo hadin kai tsakanin 'yan Najeriya domin kowane bangare ta'adancin 'yan Boko Haram ya shafa sabili da haka dole a zauna tare a nemo masalaha. Babu batun kabilanci ko addini kowa ne abun ya shafa.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.
Your browser doesn’t support HTML5