ABUJA, NIGERIA - Batun mutuwar ta Sarauniya Elizabeth tabbas wani babban lamari ne da ya girgiza duniya, kuma ya sa mutane ke sharhi daban-daban da tofa albarkacin bakinsu kan rashin sarauniyar, wacce da dama ke daukarta a matsayin uwa ga duka jama'ar duniya, lamarin dake nuna wani irin gaggarumin dattako.
A cewar fitacciyar ‘yar siyasa kuma tsohuwar kwamishinayar noma ta Jihar Kano, Dakta Baraka, tsarin shugabancin da Elizabeth ta yi a lokacin rayuwarta ya nuna shugabanci na gari da kaunar zaman lafiya.
Shi ma Ambasada Dauda Danladi wani tsohon ma'aikacin gwamnati a matakai daban-daban sannan tsohon jakadan Najeriya a kasar Pakistan, ya bayyana irin yadda yake kallon tsarin shugabancin marigayiya Elizabeth da rashinta zau kawo.
A lokacin mulkinta Sarauniya Elizabeth ta yi mu'amala da masu rike da sarautun gargajiya, kuma a cewar Alhaji Usman Ado Bayero marigayiyar tana da kyakkyawar alaka da gidan sarautar Kano.
Sarauniya Elizabeth ta mutu ne jiya Alhamis tana da shekara 96 a duniya, bayan ta shafe sama da shekaru 70 tana mulkin kasar Ingila.
Nan da kwanaki tara ne ake sa ran za a binne ta a wani kasaitaccen bikin jana'izar da aka kwashe shekaru ana shiryawa, da zai tattara manyan shugabannin kasashen duniya da dama.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5