Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saka Sarauniyar Ingila Karkashin Kulawar Likitoci


Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth II
Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth II

Shawarar likitocin na zuwa ne bayan da Sarauniyar ta kwashe yini guda a  wajen bikin kaddamar da Liz Truss a matsayin sabuwar Firaiministar Birtaniya.

Rahotanni daga fadar Buckingham na cewa Sarauniyar Ingila Elizabeth II na karkashin kulawar likitoci bayan da aka nuna “damuwa kan lafiyarta.”

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa, iyalan Sarauniyar na ta hallara a Scotland don kasancewa kusa da dadaddiyar Basarakiyar mai shekaru 96.

Wannan sanarwa na zuwa ne kwana guda bayan da Sarauniyar ta soke wani taron da za ta halarta ta yanar gizo, a lokacin da likitoci suka ba ta shawara kan cewa ta huta.

Shawarar likitocin na zuwa ne bayan da Sarauniyar ta kwashe yini guda a wajen bikin kaddamar da Liz Truss a matsayin sabuwar Firaiministar Birtaniya.

Yarima Charles mai jiran gado da matarsa Camilla na tare da Sarauniya Elizabeth a Balmoral, inda ta kan je ta yi hutu.

Bayanai sun yi nuni da cewa, shi maYarima William, babban dan Yarima Charles, na kan hanyarsa ta zuwa wajen kakarsa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG