'Yan Najeriya Miliyan 1.6 Suka Rubuta Takardun Neman Bashi Karkashin Sabon Tsari - Uzoma Nwagba

Naira

‘Yan Najeriya sama da miliyan daya ne suka mika takardar neman sabon tsarin basussuka, inji gwamnatin tarayya a ranar Talata.

WASHINGTON, D. C. - Wannan bayanin ya fito ne daga wurin Babban Manaja kuma Babban Jami’in Zastaswa Na Hukumar Kula da Kare Kayayyakin Kasuwa wato CREDICORP wanda ya ce adadin ‘yan Najeriya miliyan 1.6 ne suka mika takardun neman bashi.

A ranar 21 ga Afrilu, shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar da kashi na farko na tsarin ba da lamuni na Consumer Credit Scheme. Shirin da zai bai wa 'yan ƙasa masu aiki damar samun lamuni don sayayyar kayayyaki masu mahimmanci. Makwanni uku bayan fara shirin, shugaban na CREDICORP ya bayyana cewa yawan takardun masu nema da aka samu zuwa yanzu na da yawa.

"Ya kasance abu mai ban mamaki. Ba mu zaci yawan masu rubuta takardun bukata da kuma bayyana sha’awar hakan zai kai haka lokacin da muka fitar da EoI kamar mako guda bayan an nada nib a, "in ji shi yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television's Politics Today.

“Ya zuwa yau, muna da kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 1.6 da suka nuna sha’awarsu, suka gaya mana abin da suke yi, suka gabatar da bayanan samun kudin shiga, da kuma abin da suke bukatar yi da bashin. Ba mu yi tsammanin samun yawan mutane haka ba.

"Don haka ina ganin mutane sun kasance suna sauraron maganganun shugaban kasa kuma suna kuma fatan hakan."

Shugaban kasa ya nada Nwagba ne a matsayin shugaban CREDICORP a ranar 5 ga Afrilu don jagorantar yunkurin gwamnati mai ci na fadada wadatar lamuni na mai amfani ga 'yan Najeriya ma’aikata masu sha'awar haka.

Kimanin watanni shida da nadin nasa, ya ce ya shirya tsaf don gabatar da aikin.

Ya kara da cewa "Aikinmu ne kuma a shirye muke mu bi tsari daki daki don tabbatar da cewa mun ci gaba da kaiwa ga al’ummomin Najeriya dadan daban."