Za a ci gaba da zaben a yau Litinin a yankuna 14 daga cikin 27, wanda tun da safe za a bude runfunan zabe. Zaben da aka dade ana bata lokacin yinsa, zai cike gibin kujerun ‘yan majalisu guda 496.
Za’a ci gaba da zaben har ranakun 22 da 23 a wasu wuraren na cikin kasar. ‘Yan Kasar mazauna kasasehn waje tun a ranar Asabar suka fara kada kuri’unsu.
Ana zaton samun sakamakon zaben a farkon watan Disamba mai zuwa idan Allah ya kaimu. Kuma ba wani takamaiman labari daga jami'ai ko wata kafa ta fisbilillahi na fitowar jama’ar a jiya Lahadi, wanda aka yi hasashen ba zai wuce kashi 10 daga cikin dari ba.
Tun shekarar 2012 dai ba ‘yan majalisu a Misira, tun bayan da kotu ta soke zababbun ‘yan majalisun.
Yawanci a da ‘yan Muslim Brotherhood ne suka mamaye majalisar, jam’iyyar tsohon shugaba Masar Mohammed Morsi da aka haramtata.