Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Yi Zaben Shugaban Kasa da Na 'Yan Majalisu a Burkina Faso Watan Gobe


 Michel Kafando, shugaban Burkina Faso na rikon karya
Michel Kafando, shugaban Burkina Faso na rikon karya

Za’a yi zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisun Burkina Faso da ya sami jinkiri sakamakon juyin mulkin da bai yi karko ba. An shirya aiwatar da zaben a ranar 29 ga watan Nuwambar bana idan Allah ya kaimu. Ana kallon Zaben a matsayin baban matakin dorewar tafarkin mulkin democradiya a kasar ta Afrika ta Yamma.

A da dai an shirya yin zaben ne a ranar 11 ga watan nan da muke ciki. Amma hakan ya faskara saboda juyin mulkin da wasu sojoji masu biyayya ga tsohon hambararren shugaban kasar Blaise Compaore suka shirya amma bai yi karko ba.

An hambarar da tsohon shugaba Campaore ne a wani bori da matasan kasar suka yi bara bayan ya shafe shekaru 27 yana mulkin kasar. An kakkame na hannun damarsa bisa alaka da juyin mulkin da aka yi kwanan nan.

A yayinda aka bayyana ranar yin zabe a Burkina Faso, a kasar Gini, babban dan takarar jam’iyyar adawa na shugabancin kasar Cellou Dalein Diallo ne ya janye daga takara bisa abinda ya kira magudi.

Ya zargi gwamnatin kasar da aikata magudi a zaben na shugaban kasa. Jiya Laraba, Diallo na jam’iyyar Union for the Democratic Forces of Guinea ya bayyana haka

Ya kuma ce ba zai yarda da sakamakon zaben ba. Dama tuni sauran yan takarar shugabancin kasar suka kaucewa zabukan da za’a yi.

Shugaba Conde dai yana takarar ne karo na biyu. An kuma zabeshi karon farko ne a shekarar 2010 a zaben kasar na kashin kanta karon farko tun bayan samun ‘yancin kai shekaru 57 da suka wuce.

Jami’an jakadancin yammacin duniya sun fadi cewa akwai matsaloli a runfunan zabenranar Lahadi da kuma rikicin da ya kashe akalla mutane 3 kafin zaben.

XS
SM
MD
LG