Shi wannan zaben da aka so a hada shi da na ‘yan-majalisar dokokin kasar, wanda kuma a da aka shirya za’ayi ran 11 ga watan nan na Oktoba, ana yi mishi kallon kamar wani sabon mataki ne wannan kasar dake Afrika ta Yamma ta dauka don inganta akidar demokradiya amma kuma sai yunkurin juyin mulkin da soja masu biyayya ga hambararren shugaban kasar Blaise Campaore suka so yi, yasa ala tilas aka dage yinsa.
A ran 17 ga watan Satumba ne wannan tarzomar juyin mulkin ta jefa Burkina Faso a cikin rikicin kwannaki shidda kafin yunkurin
A cikin hirarsu da Mahmud Lalo, Dr Ja'afar Dabai na jami'ar Kampala ta kasar Uganda ya bayyana cewa, akwai alamun zaben zai yiwu kuma zai yi armashi, kasancewa kasar da kuma gwamnatin rikon kwarya tana da goyon bayan kasashen yammacin Afrika da kum sauran kasashen duniya.
Yace galibin 'yan kasar Burkina Faso da bayan gwamnatin da ta shuge suna goyon bayan bincike masababin mutuwar marigayi Thomas Sankara.
Ga Hirar Mahmud da Dr Ja'afar