Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Alfa Conde Ya Sake Lashe Zabe


Masu kada kuria sun yi layi a runfunan zaben kasar Guinea, Oct. 11, 2015.
Masu kada kuria sun yi layi a runfunan zaben kasar Guinea, Oct. 11, 2015.

Shugaban kasar Guinea Alpa Conde ya sani nasarar ci gaba da wa'adin mulki na biyu bayan samun kuri'un da zasu hana zuwa zagaye na biyu.

Shugaban hukumar zaben kasar Guinea ya sanar da shugaban kasar Alpha Conde a matsayin wanda ya sake lashe zabe domin wani wa’adin mulki na biyu, kwanaki shida bayan kamala babban zabe na kasa.

Conde ya sami kashi 58 cikin dari na kuri’un da aka kada, abinda ya hana zuwa zagaye na biyu a zaben da madugun hamayya Cellou Dlein Diallo yace an tafka magudu, ya sami kasha 31 bisa dari na kuri’un. Diallo yace damokaradiya ba a zaben. Ya kuma yi kira da a gudanar da zanga zanga domin nuna kin amincewa da sake zaben Conde.

Masu sa ido na kasa da kasa daga Kungiyar Tarayyar Turai sunce basu ga alamar magudi a zaben ba.

Conde ya kada Diallo a zaben fidda gwani da aka gudanar shekaru biyar da suka shige a zaben mulkin damokaradiya na farko da aka gudanar a kasar cikin shekaru da dama.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG