Gwamnatin Jamhuryar Kwango ta ayyana zaben raba gardama ranar 25 ga wannan wata da nufin yin kwaskwarima ga tsarin mulkin kasar da zai baiwa shugaba Denis Sassous Nguesso damar yin takara a karo na uku.
Kwaskwarimar da ake shirin yi wadda hukumomi suka bayar da sanarwa akai jiya Litinin bayan taron majalisar ministoci, zai kuma kawar da kayyade shekarun dan takarar shugaban kasa kada ya wuce 70. Yanzu Shugaba Sassou Nguesso dan shekaru 72 ne, kuma tsarin mulkin kasar na yanzu ya haramta masa sake yin takara.
A cikin watan jiya shugaban ya bada sanarwar cewa yana shirya zaben raba gardamar, mataki da ya sa dubban 'yan kasar suka hau kan tituna a Brazzaville babban birnin kasar, suna zanga zanga.
Shugaba Nguesso, yana daya daga cikin shugabannin Afirka wadanda suka janyo cacar baki da zanga zanga da suka nemi yiwa tsarin mulkin kasashensu kwaskwarima domin suyi tazarce.
Na baya bayan nan shine shugaban Burundi Pierre Nkurunziza, wanda ya sake cin zabe da yayi cikin watan Yulilamarin da ya jnayo rikici a kasar.
Shi dai shugaba Sassou Nguesso yayi juyin mulki ne a 1979, sannan ya fadi zabe a 1992. Ya sake kwace ikon kasar saboda yakin basasan da kasar ta shiga. Ya sake cin zabe a shekara ta 2002, da kuma 2009. Sai dai a duk zabubbukan biyu, 'yan hamayya sun kaurace musu.