'Yan Majalisar Dokokin Afirka Ta Kudu Sun Kada Kuri'ar Amincewa Da Rufe Ofishin Jakadancin Isra'ila

South Africa Israel Ambassador Recall

A ranar Talata ne akasarin ‘yan majalisar dokokin Afirka ta Kudu suka kada kuri’ar amincewa da kudirin rufe ofishin jakadancin Isra’ila tare da yanke huldar diflomasiyya har sai Isra’ila ta amince da tsagaita bude wuta a Gaza.

WASHINGTON, D. C. - Kuri'ar da aka kada kan kudirin da jam'iyya mai mulki ta African National Congress ta goyi bayansa, na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya gana da wasu shugabannin kasashen duniya, inda ya zargi Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Gaza tare da kai farmakin soji a yankin da aka yi wa kawanya domin neman jagororin mayakan Hamas.

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa lokacin da yake magana akan yakin Isra’ila da Hamas

Kudirin da jam'iyyar adawa ta Economic Freedom Fighters ta gabatar ya samu goyon bayan 'yan majalisar 248 yayin da 'yan majalisa 91 suka nuna adawa da shi.

Kuri'ar ta zo ne bayan da ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce ta kira jakadanta a Afirka ta Kudu, Eliav Belotserkovsky, ya koma Kudus wato Jerusalem "don tattaunawa."

Wasu masu zanga-zanga akan yakin Isra’ila da Hamas da kashe kashen Falasdinawa da ake yi

Dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu ta yi tsami sakamakon yakin Gaza. A baya Ramaphosa ya ce kasarsa ta yi amanna cewa Isra'ila na aikata laifukan yaki a Gaza, inda aka kashe dubban Falasdinawa.

-AP