Wannan ne makasudin hada wannan taro da gwamnatocin kasashen Biyu suka shirya da zummar kara karfafa hulda da cudanya tsakanin ‘yan kasuwa.
M. Sidi Mohammed, shine shugaban hukumar bunkasa kasuwancin jamhuriyar Nijer, ya bayyana cewa wannan dama ce da ‘yan kasuwar zasu hadu da takwarorinsu a maimakon yin tattaki zuwa wata kasa kafin su gamu da wasu ‘yan kasuwar.
Da dama daga cikin ‘yan kasuwar na jamhuriyar Nijer, suka fara nuna gamsuwa da takwarorin nasu bayan wannan ganawa.
Ko baya ga harkokin saye da sayarwa a tsakanin kasashen Biyu, firayin ministan kasar Tunisia, ya bukaci ‘yan kasuwa da hukumomin kasar su duba hanyoyin kafa kamfanoni da masana’antu a janhuriya Nijer, ta yadda za a bude hanyoyin saka hannayen jari ga masu bukata.
A yayin da ake gudanar da wannan babban taron hadin gwiwa, hukumomin kasuwancin kasar Nijer, da takwarorinsu na kasar Tunisia, sun rattaba hannu akan wata yarjejeniya wadda a karkashinta dukkan kasashen biyu suka dauki alwashin bada kariya ga dukkan dan kasuwar da ya sami matsala daga cikin kashen Biyu.
Daga Janhuriyar Nijer, ga rahoton Sule Mumini Barma.
Your browser doesn’t support HTML5