Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KAMARU: Gwamnati ta Zargi Bangaren Ingilishi da Kai Hare-Hare


Kasuwar Limbe da ta kone wadda aka dora alhakinta akan masu ra'ayin rikau na bangaren Ingilishi da kai wa
Kasuwar Limbe da ta kone wadda aka dora alhakinta akan masu ra'ayin rikau na bangaren Ingilishi da kai wa

Gwamnatin Kamaru ta ce kungiyar masu tsattsauran ra’ayi a bangaren kasar masu amfani da harshen Ingilishi itace take shirya kai hare-haren tada gobara a gine ginen ma’aikatun gwamnati, makamancin wanda aka kai a kasuwar garin Limbe a kwanan nan.

Wakilin Muryar Amurka Kindzeka dake can Limbe, ya ruwaito mana cewa gobarar da aka saka a kasuwar ta kara janyo kiranye-kiranye ga bukatar sabonta tattaunawa don kawo karshen yajin aiki na watanni biyar da ma’aikata ke gudanarwa a bangaren masu amfani da harshen Ingilishi.

Gobarar da ta shi a kasuwar Limbe, ta kai sa’o’I hudu tana ci a ranar Asabar, kuma shagogi hamsin ne gobarar ta kone kurmus.

Gwamnan jihar Kudu maso yammacin kasar Benard Okaila Bilai yace yan sanda suka kama wani mutum da ake zaton dan kungiyar masu akidar ballewa daga kasar ne.

Gobarar kasuwar garin Limbe ta kara nuna irin halin zaman dar-dar da ake tsakanin bangarorin Kamaru biyu masu amfani da Ingilishi wadanda basa shiri da juna.

Lauyoyi da malumma dake dake wadannan yankunan Arewa maso yamma da Kudu maso Yamma suna kan yajin aiki tun cikin watan Nuwamban bara.

Makarantu dake wadannan wurare na nan rufe kazalika harkokin kasuwanci sun yi rauni.

Masu yajin aikin suka bukatara kawo sauye-sauye ne don magance abinda suke gani a matsayin fifita harshen Faransanci bisa sauran dimbin harsunan da ake anfani da su a kasar ta Kamaru.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG