Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Zamu Yarda Da Lalata Dukiyar Al’umma Ba


Firaministan Somaliya Hassan Ali Khaire
Firaministan Somaliya Hassan Ali Khaire

Sabon firaministan kasar Somaliya , Hassan Ali-Khaire yace yana jan hankalin mukarraban gwamnatin sa domin yakar cin hanci da rashawa, kuma yayi alkawarin yaki da karya dokoki wanda yace wani abune da gwamnatin sa bazata taba lamunta ba.

A yayin da yake jawabi a wajen bikin karbar mulki a hannun tsohon Firaminista Mohammed Adan Ibrahim “Farketi” zuwa ga sabon Ministan Abdirahman Duale Beyle, Khaire ya bayyana damuwarsa kan ya kamata a tafiyar da harkokin gwamnati akan hanyoyi na gaskiya.

Ya ce “ni da shugaban kasa ba zamu yarda da lalata dukiyar al’umma ba , saboda haka zamu daura damarar yaki da duk wani wanda yake da hannu cikin Cin hanci da rashawa. Ya kara da cewa “ Duk inda cin hanci da rashawa yake to ba za a taba samun nasarar aiwatar da komai ba.”

Shekaru kusan Ashirin Kasar Somaliya itace kan gaba a kasashen da suka fi kowacce Cinhanci da rashawa kuma sunan tane na farko a jerin sunayen kungiyar Bindiddigi Kan cin hanci da Rashawa ta kasa da kasa.

A ranar Alhamis da ta gabata Firaministan ya gabatar da zaman tattaunawar sa ta farko da jami’an gwamnatin sa inda ya fadawa sabbin ma’aikatan sa kowannesu ya bayyana dukiyar da ya mallaka ga gwamnati, wani mataki na yaki da Cin hanci da rashawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG