Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra’ayoyin ‘Yan Nijer Game Da Cika Shekara Guda Na Wa’adin Mulkin Muhamadou Issoufou


Yayinda shugaban kasar Jamhuriyar Nijer Muhamadou Iossoufou ke cika shekara guda akan karagar mulki a wa’adi na Biyu, ‘yan kasar na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu akan mulkinsa, yayin da wasu ke yabawa, wasu kuma na ganin har yanzu akwai saurana rina a kaba.

‘Yan kasar da dama na ganin cewa zaman lafiya da kwanciyar hankalin da jamhuriyar Nijer ta samu wata gagarumar nasara ce da ya kamata ‘yan kasar su yaba da shi.

Jama’ar da dama sun bayyana wasu daga cikin ayyukan gyaran kasa da shugaban ke yi, kamar layin dogo da kokarin inganta tsaro da yaki da ta’addanci da kuma sauran ayyuka makamantansu.

A daya bangaren kuwa jama’ar sun koka ne akan rashin samar da abubuwan more rayuwa da gwamnatin ta alkawarta masu a lokacin da take yakin neman zabe, da kuma abinda suka bayyana a matsayin rashin imanin shugabanin da almubazaranci.

Daga Birnin Kwanni, ga rahoton da Haruna mamman Bako ya aiko mana

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG