Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Kasar Habasha Sun Sakarwa 'Yan Alshabab Yanki Mai Muhimmanci


Sojojin kasar Habasha dake yaki da ‘ya tawayen Al-shabab, sun janye daga daya daga cikin muhimmam wuraren da suke da iko, wanda ke tsakiyar gundumar Gaigudud, kamar yadda mazauna wurin ke cewa.

Mayakan al’shabab yanzu haka sun maye gurbin sojojin na kasar Ethiopia, a El-Bur, bayan da sojojin na Habasha, suka bar wannan wuri da safiyar jiya littini.

Yanzu dai wannan wuri na El-Bur, ya koma karkashin ikon Al-shabab kamar yadda shugaban gundumar yankin Nur, Hassan Gutale, yake cewa, yace kuma sojojin na kasar Habasha, basu fadi dalilin da yasa suka janye daga wannan wuri ba.

Gutale yace yaga sojojinna Habasha, kawai suna watsewa ba tare da wani bayani ba, abinda ya tilasta nasu sojojin suma su ba bar wannan wuri.

Mazauna wannan wurin suka ce sunga mayakan na Al-shabab, cikin motocin akori kura suna shigowa garin da safiyar jiya littini ba tare da sun tada hankali ba.

Wani mazauni wannan gari ya shaidawa Muryar Amurka cewa dakaru na Al-shabab sun iso cikin garin a matoci 6 kirar akori kura kuma nan take suka fara kafa tutar su.

Sai dai Gutale, ya soki lamitrin sojojin na Habasha, da mayakan na Al-shabab akan yadda suke musguna wa farar hula.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG