'Yan Jaridu da Tashe -Tashen Hankula a Duniya

'Yan Jaridu

An yi kira ga ‘yan jaridu da su kula da nauyin jama'a dake kansu domin sanin yadda ya kamata su bada rahotannin abubuwan da ke faruwa a inda ake tashe-tashen hankula a duniya don takaita harzuka al’umma da kuma kashe wutar rikici don kar ta ci gaba da ruruwa.

Masana harkokin yada labarai sun kalubalanci ‘yan jarida game da rawar da ya kamata su taka a yayin gabatar da aikinsu cikin jin tsoron Allah da kuma yin taka tsan-tsan wajen kawo rahotannin da za su kwantar da hankulan jama'a, ba tare da ruruta wutar rikici ba.

Taron da cibiyar koyar da dabarun mulki da bincike a kan zamantakewar al’umma tare da hadin gwiwar hukumar bada tallafi ta kasar Birtaniya ne suka shirya.

Wani tsohon dan jarida kuma tsohon kwamishinan yada labarai a Jihar Filato Gideon Barde, ya bayyana cewa dole ne ‘yan jarida su bada nasu gudunmawa wajen gina kasa.