‘Yan Chadi Sun Kada Kuri’ar Amincewa Da Sabon Kundin Tsarin Mulki Da Sojoji Ke Marawa Baya

Zaben Chad

Al’ummar kasar Chad sun kada kuri'ar amincewa da sabon kundin tsarin mulki da masu suka ke cewa zai taimaka wajen tabbatar da ikon shugaban mulkin sojan kasar Mahamat Idriss Deby.

An gudanar da zaben raba gardamar ne a farkon wannan watan na Disamba, inda ya samu amincewar kashi 86 cikin 100 na masu kada kuri’a, in ji hukumar gwamnati da ta shirya zaben a ranar Lahadi. Yawan masu kada kuri’ar ya kai kashi 64 cikin, in ji hukumar.

Hukumomin sojan kasar Chadi sun kira zaben a matsayin wani muhimmin ginshikin zabuka a shekara mai zuwa, wanda aka dade ana alkawarin komawa kan mulkin dimokradiyya bayan da suka kwace mulki a shekara ta 2021, lokacin da aka kashe tsohon shugaban kasa Idriss Deby a fagen daga a lokacin da ake gwabza fada da ‘yan tawaye.

Sabon kundin tsarin mulkin dai zai tabbata da kasa daya dunkulalliya, wacce Chadi ta ksance tun da ta samun ‘yancin kai, yayin da ‘yan adawar kasar suka yi kira da a samar da wata kasa ta tarayya, suna masu cewa hakan zai taimaka wajen habaka ci gaba.

Wasu ‘yan adawa da dama sun yi kira da a kaurace wa zaben, suna masu cewa gwamnatin mulkin sojan ta fi karfin ikon gudanar da zaben raba gardama.