Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Chadi Da Nijar Sun Yi Kira Ga Mali Da Ta Koma Kungiyar GS Sahel


Shugaban Kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno (R) Da Shugaban Kasar Niger Mohamed Bazoum
Shugaban Kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno (R) Da Shugaban Kasar Niger Mohamed Bazoum

Kasashen Chadi da Nijar sun yi kiran Mali ta koma kan kujerarta a kungiyar G5 Sahel domin ci gaba da yakin hadin-gwiwar da takwarorinta ke kafsawa da kungiyoyin ta’addancin yankin Sahel.

NIAMEY, NIGER - A watan Afrilun da ya gabata ne gwamnatin Mali ta bada sanarwar ficewa daga kungiyar ta G5 Sahel saboda zargin kin ba su shugabancin karba-karbar kungiyar a wani lokacin da kamun ludayi ya zo ga kasar ta Mali.

A taron manema labaran da suka kira don karkare ziyarar kwanaki biyun da shugaban kasar Nijar ya gudanar a kasar Chadi, Mohamed Bazoum da Mahamat Idriss Deby sun bayyana bukatar ganin kasar Mali ta canza matsayi watanni uku bayan ficewarta daga kungiyar G5 Sahel.

A kan wannan batu Shugaban kasar Chadi mai masaukin baki ya bayyana cewa yaki da ta’addanci wani abu ne da babu kasar da zata iya yinsa ita kadai sai an hada gwiwa domin ta’addanci ba ruwansa da iyakokin kasashe, bai kuma san kowace kasa ba.

Mahamat Idriss Deby
Mahamat Idriss Deby

Ya kuma ce za su ci gaba da tuntubar ‘yan uwansu na Mali su dawo kungiyar G5 Sahel domin ci gaba da yakin da suka kaddamar a shekarar 2013. Ya ce suna sa sa ran Mali za ta canza matsayinta.

Shugaban kasar Nijar ya yi tunatarwa akan yanayin da Mali ta fada a shekarar 2013 inda ‘yan ta’adda suka yi yunkurin mayar da ita wata daula ya kuma yi bayani akan ainihin mafarin kafa kungiyar ta G5 Sahel.

Ya ce ceto Mali daga halin da ta shiga shine ainihin dalilin kafa kungiyar G5 Sahel, idan a yau akwai matsala ana iya daukar abin a matsayin na wucin gadi, nan gaba kadan za su yi taro don duba wannan lamari.

Gwamnatin Mali na ganin wannan matsayi da ta kafe a kansa shine mafi a’ala, to amma wannan mataki ba mai dorewa ba ne har illa-ma-sha-Allah, dalili kenan ya zama wajibi mu hadu mu yi yadda kungiyar za ta farfado ta kuma amfane mu domin a baya ba a more ta ba kamar yadda ya kamata, ya kara da cewa dole ne mu gaya wa juna gaskiya.

Shugaban Kasar Niger Mohamed Bazoum
Shugaban Kasar Niger Mohamed Bazoum

Manazarta sun bayyana cewa wannan yunkuri na kasashen Chadi da Nijar abu da ya kamata kasar Mali ta yi na’am da shi ne ba tare da wata-wata ba domin yin hakan wani abu ne da ka iya maido da kimar gwamnatin ta Mali a idon duniya, inji shugaban kungiyar Voix des sans Voix Nassirou Saidou.

Wannan kira na shugaba Mohamed Bazoum da Mahamat Deby na zuwa ne a wani lokacin da tankiyar diflomasiyya ta barke a tsakanin Mali da Cote d’ivoire bayan da gwamnatin Kanal Assimi Goita ta kama wasu sojojin Cote d’ivoire 49 a ranar Lahadi da ta gabata jim kadan bayan saukarsu a filin jirgin saman Bamako, ta na mai zarginsu da yunkurin juyin mulki yayin da gwamnatin Alassan Ouattara ke cewa sojan zaman lafiya ne da ta aike domin aikin tsaro a karkashin rundunar MDD.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barm:

Kasashen Chadi Da Nijar Sun Yi Kira Ga Mali Da Ta Koma Kungiyar GS Sahel .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

XS
SM
MD
LG