Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Bikin Rantsar Da Shugaban Sojin Chadi Mahamat Idriss Itno


Mahamat Idriss Itno
Mahamat Idriss Itno

An yi bikin rantsar da shugaban sojin Chadi Mahamat Idriss Itno, wanda ya karbi ragamar mulki a watan Afrilun bara bayan rasuwar mahaifinsa.

Zai ci gaba da kasancewa kan karagar mulki na tsawon shekaru 2 lokacin da za a gudanar da babban zaben kasar.

Mahamat Idriss Itno
Mahamat Idriss Itno

Majalisar tattaunawar wanda 'yan adawa da kungiyoyin fararen hula suka kauracewa, itace ta amince da bai wa shugaba Deby damar tsayawa takara lokacin gudanar da zaben, duk da alkawarin da yayi lokacin da ya karbi mulki cewar ba zai tsaya takara ba.

Buhari da Mahamat Idriss Itno
Buhari da Mahamat Idriss Itno

Bikin dai ya samu halartar shugabannin kasashen Afirka cikin su harda Muhamadu Buhari na Nigeria.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG