‘Yan Bindiga Sun Saki Limamin Katolikan Da Suka Sace A Zamfara

Rabaran Mikah Suleiman,

Sanarwar da daraktan yada labaran shiyar Sokoto na Darikar Katolika, Rabaran Pascal Salifu, ya fitar a jiya Lahadi, tace an saki Suleiman wanda ya kasance limamin Cocin St. Raymond dake garin Dumba, a karamar Hukumar Gusau, ta jihar Zamfara, kuma yanzu yana samun kulawar da ta dace.

Rabaran Mikah Suleiman, da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi makonni 2 da suka gabata, ya shaki iskar ‘yanci.

Sanarwar da daraktan yada labaran shiyar Sokoto na Darikar Katolika, Rabaran Pascal Salifu, ya fitar a jiya Lahadi, tace an saki Suleiman wanda ya kasance limamin Cocin St. Raymond dake garin Dumba, a karamar Hukumar Gusau, ta jihar Zamfara, kuma yanzu yana samun kulawar da ta dace.

Ya kara da cewar, muna matukar farin cikin sanarda sakin Rabaran Mikah Suleiman, da aka sace a ranar 26 ga watan yunin daya wuce cikin aminci.

“Muna mika godiyarmu ga Allah saboda kariyarsa da kuma duk wanda ya taimaka da addu’a da gudunmowa a wannan lokaci na iftila’i”.

“haka kuma muha godiya ga hukumomi da dukkanin wadanda suka taimaka wajen sakin rabaran mikah. a halin yanzu yana samun kulawar data dace.”

“Don Allah ku cigaba da sashi a cikin addu’o’inku a yayin daya fara farfadowa.”

An sace Rabaran Suleiman da misalin karfe 3 daren a ranar Asabar 21 ga watan yunin daya gabata, a gidansa dake yankin damba na garin gusau.

Bayan da aka sace limamin ne, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tura tawagar zaratan jami’anta domin bin sawun wadanda suka yi garkuwa dashi tare da tabbar da kubutar da shi cikin aminci.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya tabbatar da sace limamin.